Isa ga babban shafi
Wasanni

Manchester United ta kammala sayen Farnandes daga Lisbon

Sabon dan wasan Manchester United Bruno fernandes
Sabon dan wasan Manchester United Bruno fernandes Skysport.com

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta tabbatar da kammala cinikin Bruno Farnandes daga Sporting Lisbon kan fam miliyan 47.

Talla

Farnandes dan Portugal mai shekaru 25 wanda ya takawa kasarsa leda sau 19 ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru 5 da rabi da Old Trafford, inda yayin sanya hannu kan kwantiragin ya sha alwashin ganin ya kai Club din ga nasarar lashe kofuna daban-daban.

Kafin Isar Farnandes dai dubun-dubatar magoya bayan United ne suka yi dafifi don tarbarshi dauke da hotunansa da ke yi masa barka da isowa.

Karkashin kwantiragin na Franandes bayan yimasa gwaje-gwajen lafiya da suka bayyana cikakken kuzarin da ya ke da shi, United ta bai wa dan wasan damar iya tsawaita kwantiragin a kowanne lokaci.

A cewar mai horar da kungiyar, Ole Gunnar Solskjier, tsawon lokaci suka dauka suna fafatukar ganin sun kawo dan wsan Old Trafford,

Farnandes dan wasan tsakiya mai zura kwallo, ya yi kaurin suna ne wajen wajen saurin zura kwallo da kuma tsaron tsakiya, ana ganin zai baiwa Manchester United cikakken gudunmawa la’akari da kalubalen da Club din ke fuskanta a yanzu bayan ficewa daga gasar Carabao dama kayen da ya ke fuskanta a Firimiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.