Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Manchester United ta dauko Ighalo

Dan wasan Najeriya da ya koma Manchester United Odion Ighalo.
Dan wasan Najeriya da ya koma Manchester United Odion Ighalo. Reuters Blogs

Kungiyar kwalon kafa ta Manchester United ta dauki dan wasan Najeriya Odion Ighalo har zuwa karshen wannan kakar wasanni daga Shanghai Shenhua ta kasar China a matsayin aro.

Talla

Ighalo mai shekaru 30 ya koma China daga Watford ta Ingila ne a shekarar 2017, inda ya buga wa kungiyar Changchun Yatai, kafin a shekarar da ta gabata ya kulla yarjejeniya da Shanghai.

United na da matsalar ‘yan wasa masu saka kwallo a raga sakamakon raunin da dan wasan gabanta Marcus Rashford ya samu a gadon baya, inda ake sa ran zai yi jinya na karin wata guda.

Ighalo ya ci wa Watford kwallaye 40 a cikin wasani 100 da ya buga mata.

A cikin wasanni 34 da ya buga wa kasarsa, Najeriya, dan wasan ya ci kwallaye 16, ya kuma zama dan wasan da ya fi kowa zura kwallo a raga a gasar cin kofin nahiyar Afrika ta 2019.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.