Isa ga babban shafi
Wasanni

Ronaldo ya karya tarihin Trezeguet a Juventus

Cristiano Ronaldo.
Cristiano Ronaldo. REUTERS/Massimo Pinca

Cristiano Ronaldo ya kafa tarihin ciwa kungiyar Juventus adadin kwallaye 50, a karshen mako, inda ya ci 2 daga cikin kwallaye 3 da suka lallasa kungiyar Fiorentina da su.

Talla

Nasarar dai ta baiwa Ronaldo damar karbar kabun tarihin da tsohon dan wasan kungiyar ta Juventus David Trezeguet ya shafe shekaru yana rike da shi.

Fafatawar Juventus da Fiorentina a ranar lahadi, shi ne wasa na 9 da Ronaldo ya buga a jere tare da cin kwallaye.

Yanzu haka kuma, jefa kwallaye a raga cikin karin wasanni 2 a jere suka ragewa Ronaldo, ya karya tarihin da tsohon dan wasan kungiyar Fiorentina Gabriel Batistuta ya kafa, na cin kwallaye cikin wasanni 11 na gasar Seria A da ya buga a jere, a shekarar 1994.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.