Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Trabzonspor za ta kai wadanda suka nuna wa Mikel Obi wariya kotu

John Obi Mikel, tsohon dan wasan Chelsea
John Obi Mikel, tsohon dan wasan Chelsea REUTERS/Matthew Childs

Kungiyar kwallon kafa ta Trabzonspor da ke babbar gasar kasar Turkiya ta caccaki kalaman wariyar launin fata da aka yi wa dan wasan tsakiyarta, kuma tsohon dan wasan Chelsea, dan Najeriya John Mikel Obi, biyo bayan nasararta kan Fenerbahce ranar Asabar da ta gabata.

Talla

An yi ta yi wa dan wasan mai shekaru 32 kalamai na wariyar launin fata a dandalin sadarwar intanet bayan doke Fenerbahcen 2-1 da ya kai Trabzonspor din matsayi na 3 a teburin gasar ta Turkiya.

Kungiyar ta ce ta shigar da wadanda suka aikata wannnan abin assha kara a kotu.

Kungiyar ta hau shafinta na twitter tana cewa"wariyar raunin fata dabi’a ce ta jahilai da marasa kan gado."

Shi ma abokin wasan Mikel a kungiyar Trabzonspor, Joao Pereira ya shiga shafinsa na Twitter yana cewa wariyar launin fata ba abu ne da za a lamunta ba, kuma kwallon kafa ta fi wadannan kananan mutanenmasu wannan dabi’a mai ban takaici.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.