Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Za a biya wasu 'yan kallo diyya saboda wasan da Ronaldo bai fafata ba

Cristiano Ronaldo, dan wasan Juventus da Portugal.
Cristiano Ronaldo, dan wasan Juventus da Portugal. Reuters

Wata kotu a Koriya ta Kudu ta umurci wasu masu shirya wasanni na cikin gida su biya wasu ‘yan kallo biyu diyya, bayan Cristiano Ronaldo bai fafata a wasan sada zumunta da suka shirya da Juventus ba kamar yadda suka tallata.

Talla

An shaida wa magoya baya da masoya wasan kwallon kafa cewa dan wasan gaban na kasar Portugal zai fafata a wasan sada zumunta tsakanin kungiyar K – League – all – star a watan Yulin da ya gabata, amma kuma hakan bai samu ba.

Kotu ta umurci wadanda suka shirya wannan wasan sada zumunta, wato The Fasta, su biya wasu masoyawasan kwallon kafa biyu diyyar Yuro dubu 240.

Cikin wannan kudi da zasu biya, wadannan ‘yan kallo, har da Yuro dubu 194 na tashin hankali da mutanen suka tsinci kansu a ciki, kamar yadda lauyansu Kim Min –ki ya bayyana.

An sayar da tikiti dubu 65 na wannan wasa cikin minti 3 da sanya tallar maidaauke da fuskokin Cristiano Ronaldo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.