Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Real Madrid da Barcelona sun fice daga Copa Del Rey

Lionel Messi na Barcelona da Karim Benzema na Real Madrid.
Lionel Messi na Barcelona da Karim Benzema na Real Madrid. Reuters/Albert Gea

A karon farko cikin shekaru 10 za a doka wasan karshe na cin kofin Copa Del Rey ba tare da koda guda cikin manyan kungiyoyin kwallon kafar Spain biyu masu dabi da juna ba wato Barcelona da Real Madrid, gasar da ke matsayin ta 2 mafi girma a Spain bayan Laliga.

Talla

A daren jiya Alhamis ne dai Athletic Bilbao ta yi waje da Barcelona daga gasar a wasan gab da na kusa da karshe ta hanyar zura mata kwallo guda mai ban haushi matakin da ya kawo karshen nasarar Barceonar ta kaiwa wasan karshe har sau 6 a jere cikin shekarun baya-bayan nan.

A bangare guda itama Real Madrid wadda ta sha kaye har gida a hannun Real Sociedad ta fice daga gasar ta Copa Del Rey bayan tashi wasa kwallaye 3-4 ko da dai VAR ta soke kwallon da Vinicius Junior ya zura.

Rabon da a doka wasan karshe na gasar Copa Del Rey ba tare da Barcelona ko Real Madrid ba tun shekarar 2010 inda Barcelonar ke matsayin mafi dage kofin gasar da jumullar kofuna 30 yayinda Real Madrid ke da kofuna 19.

Yanzu haka dai kungiyoyin kwallon kafa na Mirandes da Granada baya ga Athletic Bilbao da Real Sociedad su ne za su doka wasan gab da na karshe na cin kofin, kafin ware biyu cikinsu da za su doka wasan karshe tukuna a san wadda za ta dage kofin a bana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.