Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Ba mu da hurumin tilasta wa Salah zuwa Olympics - Gharib

Dan wasan Masar da Liverpool, Mohamed Salah
Dan wasan Masar da Liverpool, Mohamed Salah Reuters/Andrew Couldridge

Babban kocin tawagar kwallon kafar Masar Shawky Gharib ya ce dan wasan gaba na kasar, Mohamed Salah da kungiyarsa ta Liverpool ne ke da wuka da nama game da batun fafatawarsa a gasar Olympics da za ta gudana a Tokyo ta Japan a wannan shekarar da muke ciki.

Talla

Dan wasan gaban mai shekaru 27 yana cikin jerin ‘yan wasan Masar 50 da ake sa ran za a dama da su a gasar kwallon kafa ta Olympic, wacce wasan karshen ta ya ci karo da ranar da za a fara gasar Firimiyar Ingila ta kakar 2020/21, wato 8 ga watan Agusta.

Gharib ya ce ya fadi haka ne saboda ba zai yiwu su tilasta wa Salah shiga gasar ba.

Gasar dai ta ‘yan kasa da shekaru 23 ne amma akwai damar sanya ‘yan wasa 3 wadanda shekarunsu suka zarce haka.

Tun da farko hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta ce ba tilas bane sai kungiyoyi sun saki ‘yan wasansu da suka zarce shekaru 23 don fafatawa a gasar Olympics ta Tokyo, saboda haka Gharib ya ce ya zabi Salah ne amma hukuncin karshe na hannunsa da kungiyarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.