Isa ga babban shafi
Wasanni

Chelsea ta cimma yarjejeniyar sayen Ziyech

Hakim Ziyech.
Hakim Ziyech. REUTERS/David Klein/File Photo

Chelsea ta cimma yarjejeniya da Ajax domin kulla kwantiragi da Hakim Ziyech a  wannan kakar wasanni.

Talla

Chelsea ta tabbatar cewa, ta karbi Euro miliyan 40 a matsayin farashin dan wasan, amma ana zaton farashin zai kai Euro milyan 44 nan gaba.

A karon farko kenan da Chelsea karkashin kocinta Frank Lampard ta sayi wani dan wasa tun bayan da aka haramta mata shiga kasuwar musayar ‘yan wasa don yin cefane.

A watan Janairu Chelsea ta so sayen dan wasan mai shekaru 26 dan asalin Morocco, amma Ajax ta nuna ba za ta sayar da shi ba saboda kokarin da take na lashe gasar kasar Holland.

A bangare guda, an alakanta Chelsea da yunkurin sayen ‘yan wasa da dama a cikin watan Janairu da suka hada da Edison Cavani na PSG da Dries Mertens na Napoli.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.