Isa ga babban shafi
Wasanni

Manchester United ta killace Ighalo saboda Coronavirus

Odion Ighalo na Najeriya da ya koma Manchester United da taka leda
Odion Ighalo na Najeriya da ya koma Manchester United da taka leda Ben STANSALL / AFP

Sabon dan wasan da Manchester United ta saya dan asalin Najeriya, wato Odion Ighalo na atisaye shi kai a wani kebantaccen wuri ba tare da abokan taka ledarsa na kungiyar ba, sakamakon dari-darin cutar Coronavirus.

Talla

Dan wasan wanda ya yi tattaki daga China, makyankyasar Coronavirus, zai shafe wannan makon yana atisaye shi kadai, matakin da ake kallo a matsayin riga-kafin yaduwar cutar tsakanin ‘yan wasan Manchester United.

Kungiyar ta ce, ta dauki matakin kebe shi ne a can wani sansaninta na horaswa da ke kasar Spain saboda zai fuskacni kalubale wajen dawowa cikin kasar Ingila.

Kodayake ana sa ran Ighalo mai shekaru 30 zai kasance cikin tawagar Manchester United da za ta fafata da Chelsea a ranar Litinin a gasar firimiyar Ingila.

Ighalo ya koma Manchester United ne akan aro daga kungiyar Shanghai Shenhua da ke buga gasar Super Lig ta China.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.