Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Napoli ta yi wa Inter daya mai ban haushi

Kocin Napoli Gennaro Guttaso.
Kocin Napoli Gennaro Guttaso. © Nicolò Campo/LightRocket via Getty Images

Fabian Ruiz ne ya ci kwallo daya tilo a wasan da Napoli ta baiwa Inter Milan mamaki a wasan kusa da karshe na gasar cin kofin kalubalen Italiya, haduwar farko da kungiyoyin biyu suka yi a filin wasa na San Siro a daren Laraba.

Talla

Bayan minti 57 ne dan wasan tsakiya na kasar Spain din ya saka wannan kwallo, lamarin da ya maido da tawagar Gennaro Gattuso kan tafarkin nasara, bayan shan kaye 3-2 a hannun Lecce a karshen makon da ya gabata.

Ruiz ya yi amfani da kwallon da Giovanni Di Lorenzo ya kwaso mai daga gefe, kana ya yanke ‘yan wasan baya 3 kafin ya saka ta a ragar mai tsaron raga Daniele Padelli.

Gattuso, wanda tawagarsa ke matsayi na 11 a gasar serie A ta Italiya, ya jinjina wa ‘yan wasan nasa, inda ya ke cewa, “wannan ita ce ainihin Napoli da na sani”, sai dai ya yi gargadin cewa da sauran rina a kaba, saboda babu abin da aka tabuka, a cewarsa.

Tawagar Inter, karkashin Antonio Conte ta yi wasan babu karsashi, kwanaki bayan lallasa AC Milan 4-2 a wasan hamayya da suka gwabza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.