Isa ga babban shafi
Wasanni

Zan iya rasa aikina idan na gaza lashe gasar zakarun Turai - Guardiola

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Pep Guardiola.
Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Pep Guardiola. REUTERS/Gleb Garanich

Mai horas da Manchester City Pep Guardiola yace babu mamaki shugabannin kungiyar su kore shi daga bakin aiki, idan har ya gaza lashe kofin gasar zakarun Turai na bana.

Talla

Guardiola ya bayyana haka ne, yayinda suke shirin fafatawa a zangon farko da Real Madrid a zagayen gasar zakarun ta Turai na 2, ranar 26 ga watan Fabarairun da muke ciki.

A tarihi dai Manchester City bata taba wuce matakin kwata final ba a gasar Zakarun Turai, wanda a kakar wasa ta bara tayi yunkurin cimma hakan, amma ta sha kashi a hannun kungiyar Tottenham da a wacan lokacin ke karkashin jagorancin Pochettino.

A jimllace dai sau 4 Manchester City ke fafatawa da Real Madrid, a shekarun 2012 da 2016, inda Cityn ta sha kashi sau 2, suka kuma yi kunnen doki sau 2.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.