Isa ga babban shafi
Masarautunmu

Dalilan da suka sa Sarakuna basa sauka daga mulki a kasar Hausa kashi na 2

Sauti 10:00
rotary.org

Shirin Daga Masatun mu shiri ne da ke leka masarutun da suka shahara aduniya.Shirin na wannan makon, zai ci gaba da duba yadda wasu sarakuna a kasashen duniya, kan sauka daga gadon sarautar, don bar wa magadan su, su ci gaba da mulki kasar tasu.A shirin na makon da ya gabata, mun duba yadda a kasar Belgium, Sarki Albert II ya sauka daga mukamin shi don radin kan shi, inda ya mika wa dan shi yarima Philippe, a cikin wannan shekarar.Ita ma Sarauniya Beatrix ta Hollanda, ta sauka daga mukamin ta inda ta mika wa dan ta Willem-Alexander madafun ikon masarautar.A kasar Qatar ma sarki Hamad bin Khalifa Al Thani, ya ajiye muklamin shi ya mika wa dan shi, Sheikh Tamim a cikin shekarar ta 2013.To wannan shirin ya fara duba dalilan da suka sa sarakunan kasar Hausa, basa yarda su bar gadon sarautar tun suna da rai.Prof Aliyu Muhammad Bunza, Malami a sashen koyar da Harsunan Najiriya, a jami’ar Usman Dan Fodiyo da ke Sokoto, ya yi bayani kan wannan, don haka sai a biyo mu cikin shirin, wanda shine kashi na 2 kuma na karshe, Tare da Nasiruddeen Muhammad, don jin karin bayani.A yi saurare lafiya. 

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.