Isa ga babban shafi
Amurka

Hukumar FBI zata sake gudanar da bicinke kan yar takara Hillary Clinton

Hillary Clinton yar takara  a zaben  Shugabancin Amurka
Hillary Clinton yar takara a zaben Shugabancin Amurka REUTERS/Carlos Barria

A kasar Amurka ga duk alamu zaune bata karewa yar takara Hillary Clinton wace yanzu hukumar yan Sanda ta FBI ta bayyana cewa zata sake gudanar da bicinke dangane da wasu sakwoni ta intanet da uwargida Clinton ta aika lokacin da take rike da mukamin Sakatary harakokin wajen Amurka.

Talla

A yau juma’a hukumar ‘yan Sanda ta FBI dake kasar Amurka ta jaddada cewa zata sake gudanar da bincike dangane da wasu daga cikin sakwani da Uwargida kuma ‘yar takara a zaben shugabancin kasar Hillary Clinton ta aike da su a lokacin da ta rike mukamin sakatariyar harakokin wajen Amurka daga shekara ta 2009 zuwa 2013.

Ana dai zargin Uwargida Hillary da kaucewa ka’idojin aiki, dama aiki da na’urar ofishinta wajen tura wadannan sakwoni.

James Corney shugaban hukumar ta FBI wanda a can baya ya bukaci gani an soke bicinke ne a yau juma’a ya aike da wasika zuwa Majalisa da neman gani sun amince don bashi damar gudanar da bicinke mai zurfi a kai.

Duk da yake babu wasu bayyanai dake karo da juna dangane da wannan sabon zance, Hillary ta nemi Gafara zuwa yan kasar tareda ayyana cewa babu batun cewa ta aikata ba daidai ba a lokacin.

Sai dai abokiyar hamayyar ta Donald Trumps dake cigaba da samun koma baya ta fuskar farin jini da kuma ke yankin Manchesterd dake Hampshire ya bayyana gamsuwar sa tareda girmama hukumar yan Sanda ta FBI.

Ga duk alamu zai yi wuya ‘yar takara Hillary Clinton ta fuskanci koma baya a karatowar babban zaben kasar, kasancewar Shugaban kasar Barrack Obama, zai kaddamar da tafiye tafiye domin marawa Hillary Clinton a wadannan birane da suka hada da Arewacin Carolina,Florida da yankin Ohayio wadanda suka taimaka masa sosai a zaben da ya lashe.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.