Isa ga babban shafi
Masar

Mohammed Salah ya lashe kyautar gwarzon Afrika

Mohamed Salah Gwarzon Afrika na shekara ta 2018
Mohamed Salah Gwarzon Afrika na shekara ta 2018 RFI / Pierre René-Worms

Gwarzon dan wasan Liverpool, Mohamed Salah ya sake lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafar Afrika karo na biyu a jere a wani gagarumin biki da ya a Dakar babban birnin Senegal .Salah dan asalin Masar ya yi takarar lashe wannan kuyata ce da abokin taka ledarsa a Liverpool, wato Sadio Mane na Senegal da kuma Pierre-Emerick Aubameyang dan asalin Gabon da ke taka leda a Arsenal.

Talla

A shekara ta 2018, Salah ya jefa kwallaye 44 a wasanni daban daban da ya buga wa Liverpool, yayin da yake ci gaba da taka rawa iya gwargwado a kakar bana.

Salah ya kasance dan wasa na farko daga arewacin Afrika da ya lashe kyautar sau biyu a jere.

Wata Mujallar Kwallon Kafa ta Faransa ce ta fara bayar da wannan kyauta ta Ballon d’Or a Afrika shekaru da dama da suka shude kafin daga bisani ta mika ragama ga hukumar kwallon kafar Afrika ta CAF a tsakan-kanin shekarun 1990.

Bangaren masu bayar da horo zuwa kungiyoyin wasa, Herve Renard dan kasar Faransa wanda ya taba lashe kofin Afrika da kungiyar Zambia a shekara ta 2012 daga baya ya kuma lashe wannan kofi da kungiyar kasar Cote d’ivoire a shekara ta 2015, wanda yanzu haka yake horar da kungiyar kasar Morocco shi ya lashe wannan kyauta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.