Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa zata soma karbar harajin daga tikitan jirage

Jiragen dakon fasinjoji a Faransa
Jiragen dakon fasinjoji a Faransa @Airbus SAS

Gwamnatin Faransa ta bayyana shirin soma karbar harajin akalla euro 18 kan dukkanin tikitan zirga-zirgar fasinjojin jiragen sama daga kasar.Ma’aikatar sufurin Faransa tace za’a yi amfani da kudaden harajin, wajen samar da tsarin sufurin ababen hawa masu karancin gurbata yanayi da muhalli.

Talla

A kasar ta Faransa Ministar sufurin kasar Elisabeth Borne, tace cajin harajin zai soma aiki daga shekarar 2020, inda za’a rika karbar harajin euro daya da rabi kan tikitan sufurin jiragen sama masu saukin farashi, yayinda kuma masu tsada za’a rika cazar harajin akalla euro 18, kan kowane tikitin jirgin sama da zai yi safara a cikin Faransa da sauran nahiyar Turai.

Ministar ta kuma yi karin bayanin cewa za’a rika karbar harajin ne kan jiragen da ke fita daga Faransa ba wadanda ke shiga cikin kasar ba.

Ana sa ran cewa shirin karbar harajin na gwamnatin Faransa, zai rika sama mata kudaden shiga akalla miliyan 182 a duk shekara, domin samar da sabon tsarin amfani da abbaben hawa masu saukin gurbata muhalli, musamman jiragen kasa.

A watan Afrilu na shekarar 2018, aka soma amfani da irin tsarin harajin na Faransa a kasar Sweden, inda ake cajin harajin euro 40 kan kowane tikitin jirgin sama don amfani dakudaden wajen yakar sauyin yanayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.