Isa ga babban shafi
Wasanni

Tsohon mai horar da kungiyar kwallon kafar Switzerland ya rasu

Tsohon mai horar da kungiyar kwallon kafar Swiziland Kobi Kuhn
Tsohon mai horar da kungiyar kwallon kafar Swiziland Kobi Kuhn rfi-Hausa

Tsohon mai horar da kungiyar Switzerland Kobi Kuhn wanda ya taba taka leda da kungiyar kasar ya rasu ya na mai shekaru 76.Kobi Kuhn ya rasu a birnin Zurich na kasar Switzerland bayan fama da doguwar rashin lafiya.

Talla

Tsohon Shugaban hukumar kwallon kafar Duniya Sepp Blatter ne ya sanar da manema labarai da rasuwar tsohon mai horar da kungiyar kwallon kafar Switzerland.

Ya na daga cikin mutanen da suka yi fice a Duniyar kwallon kafa a kasar ta Switzerland,ya taba lashe kofin kasar sau shida, a lokacin da ya horar da kungiyar kasar , ya samu haskawa tareda kai kungiyar matakin na kusa da wasanni qota final a shekara ta 2006.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.