Sasanta Rikicin Siyasar kasar Madagascar

Madagascar

Le président de la transition malgache, Andry Radjoel lors d'un point de presse à son hotel à Pretoria, le 29 avril 2010.
Le président de la transition malgache, Andry Radjoel lors d'un point de presse à son hotel à Pretoria, le 29 avril 2010. Photo : stéphane de Sakutin / AFP

Ana ci gaba da gudanar da tattaunawar game da shawo kan rikicin siyasar kasar Madagascar, tare da saka ranar zabe, bayan kifar da gwamnatin kasar cikin shekarar da ta gabata.Masu shiga tsakanin rikicin siyasar kasar karkashin jagoranci tsohon shugaban kasar Mozambique Joaquim Chissano, suna gudanar da tattaunawar a birnin Pretoria fadar mulkin kasar Afrika ta Kudu.Andry Rajoelina da ya jagoranci boren kifar da Marc Ravalomanana cikin watan Maris na shekara ta 2009, mutanen biyu sun ido biyu yayin zaman sulhun, kuma lokaci zabe da ahuwa watsohon shugaban sun ci gaba da janyo tsaiko wa tattaunawar ta sulhu. Kamar yadda wasu majiyoyi daga wajen taron suka tabbatar.