South Africa

An Fara Yajin Aikin Ma'aikatan Sufuri

reuters

Dubban Ma’aikatan Sufuri akasar Africa ta kudu na yajin aiki ayau, alamarin da ya kawo cikas ga harkokin sufuri na jiragen kasa, da dukkan harkokin zirga zirgan.Yajin aikin na zuwa ne bayan an gaza yin sulhu da maaikatan.Yajin aikin ya kasance na farko cikin jerin yaje-yajen ayyukan maaikata da ake zaton za'ayi, ana saura wata daya a fara gasan wasannin kwallon kafa na cin kofin duniya.Yajin aikin na yau na iya haifar da matsaloli masu yawa a wannan kasa.Kamfanin samar da hasken wutan lantarki na kasar, Eskom yace yajin aikin ba zai shafi aikin samarda hasken wuta ba a tashoshin samar da hasken wuta na kasar.