Africa ta kudu

Shugaban matasan ANC ya bada hakuri

Photo: Reuters

An tilas ta wa shugaban matasan ja’iyyar ANC mai mulkin kasar Afrika ta Kudu, Julius Malema, bada hakuri bisa kalaman da ya yi tare da cewa zai fuskanci zaman koyon yadda ake tunkarar zafin zuciya.Jami’an jam’iyyar sun samu Malema da janyo wa ANC cece kuce, inda ya soki shugabanta kuma shugaban kasa Jacob Zuma.Malema ya soki Zuma saboda kalaman da ya yi bayan shugaban matasan ya bada goyon baya wa shirin shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe akan kwace gonakin Turawa tsiraru.An ci tarar Malema Dan shekaru 29 da hauhuwa, kudaden da suka kai Dala 1,300, tare da gargadin cewa idan ya sake nuna irin wannan hali nan da shekaru biyu, za a dakatar da shi daga cikin jam’iyyar.A cikin wata sanarwar da ya fitar, ya bada hakurin abun da ya faru tare da cewa duk lokacin da zaiyi wani abu zai nuna mutuntawa gas aura al’uma.