Madagascar

Fada Ya Barke Tsakanin Jami'an Tsaron Madagascar

Gendarme malgache dans les rues d'Antananarivo.
Gendarme malgache dans les rues d'Antananarivo. AFP / Richard Bouhet

Alhamis din nan ce fada ya kaure a Antananarivo, inda jami’an tsaron dake adawa da juna a kasar Madagasca suka yi ta harbe-harben bindigogi a tsakaninsu. Kamfanin dillancin labarai na Faransa ya ce fadan ya samo asali ne lokacin da hadin gwuiwar sojoji da jami’an tsaron sashen Gendarmerie suka far wa gungun wasu jami’an tsaron dake nuna rashin amincewa da shugabanni.Ya zuwa yanzu dai bayanin da aka samu na cewar an raunata wani farar hula guda, a wannan fafatatawa dake da nasaba da yanayin siyasar kasar, tun juyin mulkin kasar na watan maris din shekara ta 2009.