Africa ta kudu
Ma'aikatan Sufuri Sun Janye Yajin Aiki
Wallafawa ranar:
Ma’aikatan sufurin kasar Afrika ta Kudu sun janye yajin aikin da su ka shafe tsawon kwanaki 17 su na yi, wanda ya janyo cikas wa harkokin sufurin kasar baki daya.An janye yajin aikin kwanaki kalilan kafin kasar ta fara daukan nauyin gasar neman cin kofin kwallon kafa na duniya, daga ranar 11 ga watan gobe na Yuni zuwa ranar 11 ga watan jibi na Yuli.