An bude taro karo na 25 tsakanin Faransa da Afrika
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Kasar Faransa ta bayyana shirin bunkasa kasuwanci da kasashen nahiyar Afrika, kamar yadda ta battar yayin bude taro karo na 25 tsakaninta da kasashen nahiyar.Shugaban kasar ta Faransa, Nicolas Sarkozy mai masaukin baki, ya tabbatar da haka a gaban shugabannin nahiyar 38 da shugabannin kungiyoyin ‘yan kasuwa 250 daga nahiyar.Shugabannin gwamnatocin mulkin sojan kasasashen Guinea Conakry da Janhuriyar Niger suna cikin masu halartan taron.Kasar Madagascar ba ta cikin wadanda aka gayyata, yayin da kasar Zimbabwe ba ta tura wakilai ba, bayan da Faransa ta fitar da sunan shugaba Robert Mugabe daga cikin masu halarta.A cikin jawabin bude zaman taro shugaban kasra ta Faransa Sarkozy, ya nuna mahimmancin da nahiyar ta Afrika ta ke da shi.