FARANSA

Afrika ta dace da kujerar Majalisar Dinkin Duniya

Shugaban kasar Faransa, Nicolas Sarkozy, yace lokaci yayi da dole a dama da kasashen Afrika, a harkokin siyasar duniya.Yayin da yake jawabi a taron kasar Faransa da kasashen Africa, shugaba Sarkozy yace, ya dace Africa ta samu gurabe a kwamitin Sulhu, dan tofa albarkacin bakin ta.Shugaban yace, babu yadda za’a tattauna matsalolin duniya, ba tare da kasancewar wakilan Africa a wurin ba.Daga nan sai yayi alkawarin wuce gaba, wajen ganin an kawo sauyi a kwamitin Sulhun, da zaran Faransa ta karbi ragamar jagorancin kasashe takwas masu karfin tattalin arzikin masana’antu, wato G-8 da kuma G- 20 a cikin shekara mai zuwa.