NIjar

Hirar da shugaban kasar jumhuriyar Nijar, Janar Salou Djibo ya yi da rfi.

Le président Salou Djibo, à Niamey, le 27 avril 2010.
Le président Salou Djibo, à Niamey, le 27 avril 2010. Sia Kambou/AFP

RFI:Shugaba tun lokacin juyin mulkin ranar 18 ga watan Februyeru,a karfe 12 na rana ,ba a ji muryarka ba da yawa.S.D.:Ba karfe 12 ne ba, karfe daya ne.Yanayin ya kassance kussan kasar Nijar ta shiga cikin wani hali na yamutsi ta fanin siyasa.Mu kuma, mu ka kuduri dokar matakai ,ta hanyar sadakar da kai ,domin kadda lamura su cabe cikin kasa.RFI:Ka na cewa kun sadakar da kan ku,amma soji kalilan ne su ka kassance a cikin juyin mulkin? S.D.:Sadakar da kai ai sadakar da kai ne.Mu sadakar da kai domin kasar mu,abun da dukan wani soji ya yi rantsuwa a kai kenan.RFI:Wane abu ne da Shugaba Tanja ya yi da ya sa ku ka doki wanan mataki?Maganar hita daga kungiyar CEDEAO musali? S.D: Wanan ba ni iya cewa komi a kai, sabili da ni soji ne ,ba dan siyasa ba.Ban san abun da ya ke yi ba a fadarshi.RFI:Ko mi ya sa ku ka doki wanan mataki? S.D.: Wanan abu ne da kowa ke iya gani karara.Lamarin siyasa ya kai inda ake tautaunawa da kungiyar CEDEAO,Kungiyar Tarrayar Afrika ,Kungiyar Tarrayar Turai da dai sauren su.Idan ba a magance lamarin ba, komi zai bace baki daya.Shi ya sa mu ka kawo gyara kuma a kan daidai. RFI:A na iya cewa ba a samu mace-mace ba? S.D.:Ba a samu kasha-kashe ba ,ko rauni ba a samu ba a cikin mambobin gwamnatin.RFI:A jajirin ranar ne ku ka doki niyar kai falmakin ko ko a yaushe ne? S.D.:A karfe daya ne mu ka doki kudurin kai hari a cikin mintoci 25 zuwa 30 komi ya kammalla.RFI:A karshe ne ku ka doki mataki? S.D.:Mu yi niya babu gudu ba bu jaa da baya.RFI: Sabili da taron ministoci kenen ana iya cewa wata damace ta samu gareku? S.D.:Ba haka ba ne, faduwa ce watakilla ta zo daidai da zama.Mun yi niyar domin maido da demokaradiya a cikin kasa,sa bo da haka, ni a gani na ba juyin mulki ba ne aka yi, gyara ne.RFI:Kamar yadda ka furuta so tari, maido da demokaradiya ne nuffin ku,ba bu ko mutun guda da ga cikin mambobin majalasar ku da zai tsaya takara a zabe mai zuwa? S.D.:Babu bukatar sake aza wanan tambaya ,akoye ayoyin doka da dama da su ka haramtama Praministan gwamnatin rukon kwarya da dukan wani minista na rukon kwarya tsayawa takara a zabe mai zuwa.RFI:Dukan abukan tafiyar ku sun amunce? S.D.:Dukan mu tafiyar guda,maganar mu guda.RFI:Komitin tuntubar juna ya mika maku jadawalin zabe ,ko za ka iya mumu Karin bayani a kai? S.D:Ni ba shugaban hukumae zabe ta kasa ne ba ,abun da zan ce shi ne, rukon kwarya zai doki waadin watani 12.RFI:Komi zai kare daga bakin ranar cikon shekara guda da ku ka doki mulki? S.D.:Lalle azimu ,haka muke sa rai daga bakin 1 gawatan Marise na shekara ta 2011.RFI:Da ga bakin wanan rana ta 01 ga watan Marise ka tsaya daga zama shugaban kasa kenan ? S.D.:Tabat wanan haka neRFI:To me za ka yi S.D.:Zan tsaya kan ko wace bukatar kasa, in ta taso.RFI:Ko za a gudanar da wani bincike kaffin karshen mulkin rukon kwarya? S.D.:Kan maganar bincike ,tuni aka fara sati guda kenan.Kuma gurin mu,ba shi ne na ruffe wani ko kuma wani a daure ba ,gurin mu shi ne na maido da kudin da aka doka daga cikin aljihun gwamnati a cikin kaida ba.RFI: Kowa zai iya tsayawa zabe ? S.D.:Bamu ba ne za mu tsaida wanan magana,dokokin kasa ne za su tsaidawa.RFI:Me ke makowar shugaban kasa Tanja a halin yanzu? S.D.:Yan Nijar ne za su sanar da makomar shi,a yanzu haka ba gidan kasso ya ke ba ,ya na tsare ne.RFI:Kenan kotu za ta yi aikin ta ? S.D:Kotu za ta yi aikinta a nan.