Najeriya
Nigeria zata binciki kisan Yan kasar a Libya
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Gwamnatin Nigeria tace tana gudanar da bincike kan zargin kashe wasu Yan kasar, da Gwamnatin kasar Libya tayi.Ministan kasa a ma’aikatar yada labarai da sadarwa, Labaran Maku, ya baiyana haka, inda yake cewa tuni dai sun sun kaddamar da bincike, dan gano wadanda aka kashe.Ministan yace, da zaran sun tabbatar da zargin, zasu dauki matakin da ya dace.Rahotanni sun nuna cewar, Gwamnatin Kasar Libya, ta aiwatar da hukuncin kisa kan wasu Yan kasashen Africa 18, cikinsu harda Yan Nigeria da Janhuriyar Niger, yayin da wasu da dama ke jiran aiwatar musu da kisan.