Nigeria

Dalilin da ya sa ban kori hafsoshin soji ba -Jonathan

Shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan, ya bayyana dalilan da ya bai kori hafsoshin sojin kasar, bayan ya karbi ragamar tafi da Nigeria, sakamakon rasuwar shugaba Umaru Musa Yar’adua.Yayin da yake jawabi a Ibadan, shugaba Jonathan, yace ya fuskanci matukar matsin lamba daga bangarori da dama, cewa idan bai kori hafsoshin ba, to lalle zasu hambarar da shi.Shugaban yace, yayi nazarin bukatun, sai yace daukar matakin ba zai taimaki Nigeria ba, a cikin wannan lokacin, domin zaman lafiyar kasar, yafi bukatar mutum guda, saboda haka ya kyale su a mukamansu.Shugaba Jonathan ya yaba da rawar da sojin suka taka, na dorewar demokradiya, inda ya bukaci Yan Siyasa da su maida hankali wajen taka rawar da ta dace da su.