Somaliya

Mutane 28 sun rasa rayukansu a wani sabon fada

Photo: Reuters

Akalla mutane 28 suka rasa rayukansu, yayin da 60 suka samu raunuka, sakamakon fafatawar da akayi, tsakanin dakarun Gwamnatin Somalia, da kuma Yan kungiyar Al Shabaab, a birnin Mogadishu.Fadan ya biyo bayan kaddamar da hare hare, da dakarun Gwamnati suka yi, da sojojin da suka samu horo a kasar Habasha.Sojin dake samun goyan bayan dakarun kasashen Afrika, masu aikin samar da zaman lafiya, na kokarin kwace sassan birnin dake hannun kungiyar Al Shabaab.Yanzu dai haka, kungiyar Al Shabaab ce, ke rike da mafi yawan sassan birnin.