Demokradiyyar Congo

Kasar Congo ta dakatar da shugaban rundunar Yan Sandan kasar

AFP / Marco Longari

HUKUMOMIN Kasar Janhuriyar Demokradiyar Congo, sun dakatar da shugaban Rundunar Yan Sandan kasar, da bada damar gudanar da bincike, kan kisan gillar da aka yiwa wani fitaccen mai rajin kare Hakkin Bil Adama, Floribet Chebeya.An dai kashe jami’in ne makon jiya, bayan Yan Sandan sun gaiyace shi, inda aka yar da gawar sa a bayan gari.Tuni Majalisar Dinkin Duniya, tare da manyan kasahsen dake baiwa Congo agaji, irinsu Britaniya, Faransa da Amurka, suka bukaci a gudanar da bincike.