AU-Uganda-Sudan

Uganda taki gaiyatar shugaba al Bashir taron kungiyar kasashen Afrika

shugaba Umar Hassan al Bashir na Sudan
shugaba Umar Hassan al Bashir na Sudan AFP / Ashraf Shazly

SHUGABAN Kasar Uganda, Yoweri Museveni, yace ba’su gaiyaci shugaba Umar Hassan al Bashir na Sudan ba, wajen taron kungiyar kasashen Africa ta AU, da za’ayi a cikin kasar.Fadar shugaban tace, wasu jami’an Gwamnati na iya wakiltar Sudan, a taron, wanda ake saran shugaban kotun dake hukunta aikata manyan laifufuka zai halarta.Kasar Uganda, na daya daga cikin kasashen da suka sanya hannu wajen kafa kotun dake hukunta manyan laifufuka na Majalisar Dinkin Duniya, dake neman kama shugaba al Bashir, dan ansa laifufukan yaki a Yankin Darfur.Jakadan Sudan a Uganda, Hussein Awad Ali, yaki amincewa da matakin, inda yace ya kamata Uganda tayi aiki da kudirin kungiyar kasashen Afrika, na kin aiwatar da umurnin kotun.