Sudan

Taron tarrayar Afrika,halartar shugaban Sudan

法广

      Hukumomin kasar Ouganda sun sake dawowa kan maganar hallartar shugaban kasar Sudan ,Umar Hassan El- Bashir,a taron tarrayar Afrika a kasar.      Taron dai zai gudana a karshen watan Jully a Garin Kampala.Da farko an furuta cewa shugaban kasar ta Sudan ba zai hallarci taron ba sabili da sammacin da kotun duniya ta bada na a kamoshi ruwa a jallo.        Hukumomin kasar Ouganda ,sun ce ba su gaiyace shi ba .A yanzu kuma sun furuta cewa, sun aika mashi goron gaiyata ,bayan da kasar Sudan ta yi barazanar kira ga kungiyar tarrayar Afrika da ta dage taron zuwa wata kasa ta daban.        A dai taron kasar Libiya a shekara ta 2009 shugaban kasar ta Sudan bai samu hallarta ba,sabili da wanan lamari.