Najeriya

Kotu ta daure tsohon shugaban hukumar yaki da miyagun kwayoyi

WATA Kotu a Lagos, ta daure Tsohon shugaban hukumar dake yaki da masu shad a fataucin miyagun kwayoyi, Alh Bello Lafiaji, shekaru 16 a gidan yari, saboda samun sad a laifin hada baki dan karbar cin hancin Euro 164,300.Mai shari’a, Olusola Williams, yace ya gamsu da shaidun da aka gabatar masa, saboda haka ya daure Lafiaji, tare da wani hadiminsa.