Kenya

Anyi aiki fida akai wa PM Odinga

Raila Odinga
Raila Odinga Reuters

Anyi aikin fida akai wa Prime Ministan kasar Kenya Raila Odinga, yau Talata, bayan garzayawa da shi asibiti, kamar yadda jami’ai suka tabbatar.A cikin wata sanarwa shugaban asibitin birnin Nairobi, Cleopa Mailu ya bayyana cewa, PM Odinga ya buga kai da cikin mota makonni da suka gabata, kuma bayan gudanar da bincike an gano hakan ya janyo ciwon da yake ji.Likitin da yayi aikin, ya ce PM Odinga, dan shekaru 65, yana farfadowa, kuma an shawarce shi ya huta, kafin komawa bakin aiki.Odinga yana rike da mukamun PM kasar ta Kenya tun cikin watan Afrilu na shekara ta 2008, bayan yarjejeniyar raba madafun iko, samakon rikicin da ya biyo bayan zabe watan Disamba na shekara ta 2007.