SUDAN
An Kirkiro da hukumar da zata gudanar da zaben raba gardama
Wallafawa ranar:
Majalisar dokokin kasar Sudan ta kirkiro hukumar da zata gudanar da zaben raba gardama wa yankin kudancin kasar mai arzikin man fetur.Watanni shida suka rage a gudanar da wannan zabe, kamar yadda aka tsara cikin yarjejeniyar zaman lafiya ta shekara ta 2005, data kawo karshen yakin basasan kasar tsakanin kuda da arewa.Zaben na raba gardama shi zai tantance makomar yankin na kudanci ko ya ci gaba da kasancewa tare da hadaddiyar Sudan, ko kuma ya balle.