Uganda

Uganda ta kara yawan dakaru kusa da iyaka da Demokaradiyar Congo

Reuters

Rindinar sojan kasar Uganda ta kara yawan dakaru dake kan iyaka da kasar Janhuriyar Demokadariyar Congo, kwana daya bayan harin ‘yan tawaye ya hallaka mutane biyar.Wata kungiyar ‘yan tawayen Uganda mai suna Allied Democratic Forces (ADF), ta kai hari kan garin Mutwanga mai nisan kilo mita 50 daga kan iyaka, kamar yadda ma’aikatar tsaro ta tabbatar.Kungiyar ‘yan tawayen dake samun mafaka cikin Conga, ta dauki tsawon lokaci tana gwagwarmaya da makamai.