Guinea

Jama’a sun yi zanga-zanga yau a kasar Guinee

( Photo : RFI/ Laurent Correau )

 Bayan zaben shugaban kasa ,a kasar Guinee Conakry,magoya bayan dan karar shugaban cin kasar, Sidya Toure da ya kassance na 3, a cikin jeran yan takara ,sun gudanar da zanga-zanga.Yan sanda sun hasu shiga a cikin tsakiyar birnin domin cigaba da da zanga-zangar.  Masu goyon bayan dan takara ,sun furuta cewa ,an tabka magudi a zaben da ya gudana a ranar 27 ga watan da ya gabata.Dan takara Sidya Toure ya samu kishi 15 da digo 60 ne kawai a cikin 100.          A dai ranar 18 ga wanan watane ,za a gudanar da zaben zagaye na 2. Wani tsohon Praministan kasar Cellou Dalein Diallo ya kassance da kishi 39 da digo 72 cikin 100 sai kuma Alpha Conde rikaken dan adawar kasar da ya samu kishi 20 da digo 67 cikin 100.