Africa ta kudu

Desmond Tutu Zai Jingine Harkoki Ya Koma Ga iyali

Archbishop Desmond Tutu
Archbishop Desmond Tutu Photographer: Elke Wetzig

Archbishop Desmond Tutu na kasar Afrika ta kudu ya bayyana niyyarsa ta jingine dukkan wasu harkoki na jama'a bayan kwashe shekaru masu yawa a nata gwagwarmaya dashi.Desmond Tutu wanda ya taba samun kyauta da ake kira Nobel laureate ya fadawa taron manema labarai haka yau a chuchin st. George Cathedral dake Cape town.Yace a ranar bakwai ga watan Oktoba zai cika shekaru 79 saboda haka lokaci yayi na ajiye dukkan ayyuka ya koma don ya tsuguna cikin iyalansa.Yace abin nufi shine ya koma ya zauna tare da iyalinsa maimakon tutur yana halartan taruka a wurare daban daban.Desmond Tutu ya auri matar sa Leah cikin shekara ta 1955 kuma suna da ‘ya’ya hudu