GABON

Gabon na bikin cika shekaru 50 da samun yancin kai

kasar Gabon
kasar Gabon (Photo : AFP)

YAU ne kasar Gabon ke bukukuwan cika shekaru 50 da samun Yancin kai, daga hannun Turawan mulkin mallakan kasar Faransa.Yayin da ake gudanar da bikin, shugaban kasar, Ali Bongo, ya bayyana bada kwangila ta Dala biliyan hudu da rabi, wa wasu kanfanoni dan fara noman kwarar manja, samar da hanyoyi, da kuma gidaje 5,000 ga marasa karfi a cikin shekaru biyu.Ana saran kwangilar zata samar da aikin yi wa mutane sama da 50,000 a cikin kasar.Kasar Gabon na fama da raguwar man fetur da take fita da shi zuwa kasashen waje, dan samun kudin shiga. Ana saran shugabanin kasashen duniya da dama zasu halarci bikin nay au, cikinsu harda shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan.