Congo

Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar da bincike kan fyade wa mata 150

Janhuriyar Demokradiyar Congo
Janhuriyar Demokradiyar Congo no man's land

MAJALISAR Dinkin Duniya ta kaddamar da binciken zargin yiwa mata sama da 150 fyade, da ake zargin Yan Tawayen Congo da aikatawa.Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki Moon, yace zai tura wasu manyan jami’ansa biyu dan gudanar da bincike akai, yayin day a bukaci kasar Congo da ta gudanar da nata binciken.Rahotanni na nuna cewar, Yan Tawayen sun yiwa mata da yara maza sama da 200 fyade na kwanaki hudu, a garin Luvungi, bayan sun kai hari.Garin da nisan mile 10 tsakaninsa da sansanin dakarun samar da zaman lafiya, na Majalisar Dinkin Duniya.Tawagar Kungiyar kare Hakkin Dan Adam, dake Yankin, ta tabbatar da aikata fyaden wa akalla mata 154, da Yan Taawayen FDLR da kuma Yan Tawayen Mai Mai suka aikata a kauyen Bunangiri