Somaliya-Uganda

Kungiyar al Shabaab ta kashe sojojin Uganda hudu

sojojin kungiyar al Shabaab
sojojin kungiyar al Shabaab Photo: Reuters / Feisal Omar

WANI Harin kungiyar al Shabaab a fadar shugaban kasar Somalia, yayi sanadiyar kashe dakarun samar da zaman lafiya na kungiyar kasashen Afrika hudu.Kakakin kungiyar kasashen Afrika, dake kula da aiyukan samar da zaman lafiya, Barigye Ba Hoku, yace sojin da aka kashe Yan kasar Uganda ne.Uganda da Burundi sun girke sojoji 6,300 a cikin kasar ta Somalia, mai fama da tashin hankali, ganin yadda kungiyar al Shabaab ke neman hambarar da Gwamnatin rikon kwaryar kasar, a karkashin shugaba Sheikh Sharif Ahmed.Shuagban kasar ya nemi taimakon kasashen duniya, dan magance matsalar kungiyar al Shabaab, dake barazana wa daukacin kasar.