Majalisar Dinkin Duniya-Somaliya

Kungiyar al Shabaab ta kashe fararen hula 230

Birnin Mogadishu
Birnin Mogadishu AFP/Abdurashid ABDULLE

HUKUMAR kula da Yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, tace fararen hula 230 aka kashe a kasar Somalia, a cikin makwanni biyu da suka gabata.Kakakin hukumar, Melissa Fleming, tace mutane sama da 400 kuma sun samu raunuka, a hare haren da Kungiyar al Shabaab ta kaddamar a Mogadishu.Wata mata da ta tsere daga birnin, tace babu abinda mutum yake gani sai gawawaki a tituna.