Najeriya

Nuhu Ribadu Da Bukola Saraki Sun Shiga Takaran Shugabancin Kasar

Tsohon shugaban hukumar yaki da masu karya tattalin arzikin Najeriya Nuhu Ribadu
Tsohon shugaban hukumar yaki da masu karya tattalin arzikin Najeriya Nuhu Ribadu RFI Hausa

Tsohon Shugaban Hukumar Yaki da masu karya tattalin arzikin Najeriya, Nuhu Ribadu ya bayyana shirin sa na hawa kujeran Shugabancin Najeriya.Nuhu Ribadu wanda ya koma Najeriya daga gudun hijira cikin watan shida na wannan shekaran, ya fadi cewa zai tsaya takaranne karkashin jamiyyar Action Congress of Nigeria (ACN).Ya fadawa manema labarai a Abuja cewa zai shiga cikin ayarin mutanen dake niyyar kawo gyara a Najeriya.Haka nan kuma Gwamnan Jihar Kwara Bukola Saraki ya bayyana cewa zai tsaya takaran Shugabancin kasar karkashin jamiyyar dake mulkin kasar PDP.Ta yanar gizo ne Gwamnan ya bayyana niyyar sa na tsayawa takaran