Cote d’ivoire
Cote-D’Ivoire,Gbagabo na zargin jakadun kasashen waje da yin makarkeshiya
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Shugaban Kasar Cote- D’ivoire, Laurent Gbagbo, ya zargi Jakadun kasashen duniya, da yunkurin hada shi da sojin kasar, dan ganin sun juya mashi baya.Sabon ministan harakokin cikin gidan kasar na bangaren Laurent Gbagabo, Emile Guiriolou, ya ce suna da bayanan dake nuna wasu Jakadun kasashen waje na janyo ra’ayin manyan sojin kasar dan su juya baya ga shugaba Gbagabo, abin da ya ce Gwamnatinsu ba za ta amince da shi ba.Mininstan kasar Franshi , Henri de Raincourt, ya yi watsi da zargin, a Burkina Faso, inda ya ke cewa shugaban da suka amince da shi shine Alassane Ouattara.