Sudan

Shugaban ‘yan tawayen kudancin Sudan ya raba gari da gwabnatin kasar

Omar al-Bashir shugaban kasar Sudan
Omar al-Bashir shugaban kasar Sudan Reuters

Shugaban ‘yan tawayen yankin Darfur, Minni Minnawi, da ya sanya hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiya da Gwamnatin kasar, ya zarge ta da kasa aiwatar da yarjejeniyar.Minnawi ya ce kudancin Sudan zai kada kuri’ar samun Yancin kanshi a shekara mai zuwa, wanda zai bar Sudan ta cigaba da zama a matsayin rusashiyar kasa.Yanzu haka Minnawi ya koma kudancin Sudan, bayan ya yi watsi da ofishinsa a Khartoum na baiwa shugaban kasa shawara.