Akalla mutane hudu sun hallaka cikin rikicin Cote d'Ivoire
Wallafawa ranar:
Fada ya balle tsakanin dakarun dake biyayya wa Laurent Gbagbo da masu zanga zangar goyon bayan Alassane Ouattara da kasashen duniya suka hakikance ya laseh zaben da ya gabata, abunda ya janyo mutuwar akalla mutane hudu.Anji karar makamai yayin da masu zanga zangar ke macin zuwa gidan telebijin na kasar a birnin Abidjan.Magoya bayan Ouattara sun mamaye manyan titunan birnin inda suek zanga zanga, domin bin umurninsa na neman kawar da Gbagbo daga madafun iko ta hanyar zanga zanga.Dakarun dake biayya wa Laurent Gbagbo sun kai ruwa rana da masu masu zangar dake nuna goyon baya wa Alassane Ouattara, abun da ya janyo jikata akalla mutane uku.Ouattara wanda duniya take mara wa baya kan cewa shine mutumin da ya lashe zaben watan Jiya, amma daga bsa kotun tsarin mulki da ‘yan kanzagin Gbagbo suka mamaye ta soke kuri’un wasu mazabu na arewaci tare da aiyana Gbagbo a matsyain wanda ya lashe zaben.Masu zanga zangar na macin zuwa babbar telebijin ta kasa yayin da sukayi arangama da jami’an tsaro.Tuni Babban jami’in Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya nuna damuwa da yanayin da ake ciki, wanda zai iya kazancewa ko yaushe.Kotun duniya mai hukunta masu laifukan yaki ta bayyana saka ido kan kasar ta Cote d’Ivoire, domin huunta duk wanda zai janyo rikicin da zai hallaka mutanen da basu san hawa ba bare sauka.