Cote d’ivoire

An kara tsakanin masu zanga zanga da dakarun Cote d’Ivoire

Laurent Gbagbo da Alassane Ouattara shugabannin kasar Cote d'Ivoire biyu masu adawa da nuna
Laurent Gbagbo da Alassane Ouattara shugabannin kasar Cote d'Ivoire biyu masu adawa da nuna (© Reuters/Montage : RFI)

Dakarun dake biayya wa Laurent Gbagbo sun kai ruwa rana da masu masu zangar dake nuna goyon baya wa Alassane Ouattara wanda aka yi imanin ya lashe zaben da ya gabata, abun da ya janyo jikata akalla mutane uku.Ouattara wanda duniya take mara wa baya kan cewa shine mutumin da ya lashe zaben watan jiya na Nowamba, amma daga bisa kotun tsarin mulki da ‘yan kanzagin Gbagbo suka mamaye ta soke kuri’un wasu mazabu na arewaci tare da aiyana Gbagbo a matsyain wanda ya lashe zaben.Masu zanga zangar na macin zuwa babbar telebijin ta kasa yayin da sukayi arangama da jami’an tsaro.Tuni Babban jami’in Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya nuna damuwa da yanayin da ake ciki, wanda zai iya kazancewa ko yaushe.