Najeriya

Ban Ki Moon ya nuna damuwa kan rikicin Plato a Najeriya

Najeriya wani lokaci na juyayi
Najeriya wani lokaci na juyayi (Photo: AFP)

Babban magatakarda na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki Moon, ya bayyana kaduwar sa kan barkewar wani sabon rikici a Jihar Plato da ke tarrayar Najeriya.Sabon rikicin da ya lakume rayuka sama da 50.Ban Ki Moon,ya yi Allah wadai da harin bama- baman da aka kai a shiyar Gada Biyu, Anguwar Rukuba da kuma Amigo Junction, ya goyi bayan matakan da hukumomin Najeriya ke dauka, na magance wanan matsalar.A jawabin da Gwamnan Jihar, Jonah Jang ya yi a karshen mako, ya zargi Yan adawa da kai harin da tunzura Musulmi da Krista sake fada a tsakaninsu.