Niger

Nijar :Ko dada Tsohon shugaban zai gurfana a gaban kotu ?

Tsohon Hambararen shugaban kasar jumhuriyar Nijar Mamadou Tandja
Tsohon Hambararen shugaban kasar jumhuriyar Nijar Mamadou Tandja AFP

A jumhuriyar Nijar magoya bayan tsohon shugaban kasar ,Mamadou Tandja sun ce ba adalci a ce ya gurfana a gaban kotu.Tun dai da hukumominrukon kwarya a kasar jumhuriyar Nijar su ka sanar da cewa an hida rigar kariyar ga tsohon shugaban kasar Mamadou Tandja,magoya bayan shi su ka fara tsokacin cewa da walaki goro cikin miya.Mahamadou Aboubakar dan Dubai da ya jagorenci tawagar ta zarce a lokacin tsohon shugaban kasar ya kalubalanci maganar gurfanar da shugaban agaban kotu.A cikin wata hirar da sashen hausa na rfi ,ya furuta cewa gurfanar da tsahon hambararen shugaban a gaban kotu ba adalci ba ne.Daga nasu bangare ba za su rufe baki bas ai dai kasa ta game da sama.Kuma su na da niyar gudanar da zanga-zanga ta nuna kin amuncewar su da wanan lamari na gurfanar da tsohon shugaban a gaban kotu.