Najeriya

Jonathan zai nada mai bashi shawara kan Ta’addanci a Najeriya

Shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan
Shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan REUTERS/Afolabi Sotunde

Shugaban kasar Najeriya Goodluck Ebele Jonathan ya bayyana kudirin nada mai ba shugaban kasa shawara kan ta’addanci don kara inganta sha’anin tsaro a kasar, musamman hare haren bama baman da ake wa gwmanatinsa barazana da su da ke lakume rayukan al’ummar kasar.Wannan sanarwar na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban ke taron gaggawa da jami’an tsaron kasar sanadiyar harin Abuja na biyu da aka kai a wata kasuwar mami kusa da barikin sojoji a jajibirin sabuwar shekara da kuma harin jajibirin kirsimeti a garin Jos.A mako mai zuwa ne dai shugaba Jonathan zai nada wanda zai ba shi shawara kan ta’addanci, kamar yadda mai Magana da yawunsa Ima Niboro ya shaidawa manema labarai.Tuni dai wata kungiya ta Jama’atu Ahlus-Sunnah Lidda’Awati Wal Jihad da ake kira Boko Haram ta dauki alhakin kai harin Jos. Sai dai kuma har yanzu babu wanda ake tuhuma da kai harin Abuja tun bayan da MEND ta nisanta kanta da kai harin.