Najeriya

MEND ta nisanta kanta ga daukar alhakin harin Abuja

kasuwar da aka kai harin a Abuja
kasuwar da aka kai harin a Abuja AFP PHOTO/WOLE EMMANUEL

Kungiyar da ke fafutikar yakin ‘yancin Niger Delta wacce ta yi ikirarin daukar alhakin kai harin kasuwar mami a Abuja, ta fito ta nisanta kanta daga wannan ikirarin a wani sakon Email ta yanar gizo da kungiyar ta yada.Harin bom din wanda ya ya tashi a dai dai kasuwar da mutane ke hada hadarsu kusa da barikin soja, harin ya yi sanadiyar mutuwar mutane hudu tare da raunana mutane da dama.A yanzu haka dai babu wadanda ake zargi da kai harin kamar yadda shugaban kasar, Goodluck Jonathan yace har yanzu babu wadanda ake tuhuma da aikata kai harin.Wannan harin shi ne na biyu tun bayan harin 1 ga watan Octoba da kungiyar MEND ta dauki alhakin kai wa lokacin da Najeriya ke bukin cika shekaru hamsin da samun ‘yancin kai wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 10.