Niger

Kididiga kan zaben shugaban kasa a jumhuriyar Nijar

Wani kanfani da ake kira Omega Intelligency, da ya kware wajen bincike ,lissafi da kididiga,ya gano da cewa a zaben shugaban kasa da zai gudana a kasar jumhuriyar Nijar,Mahamadou Issoufou na jama’iyar PNDS -Tarrayar zai kassance na Farko da yawan kuri’u kishi 46 cikin dari,Mahamane Ousman na CDS-Rahama na 2 da yawan kuri’u kishi 26 cikin dari,a yayin da Cheiffou Amadou na RSD-Gaskiya zai kassance na 3 da yawan kuri’u kishi 24 cikin dari. Binciken ya nuna da cewa Cheiffou Amadou zai taka rawa ta massanman kan ganin wanda zai kassance shugaban kasar Nijar a shekara ta 2011.Kanfanin na Omega mai cibiya a binin Yamai na jumhuriyar Nijar ,ya gudanar da wanan bincike ne ta hanyar kira kuma jin ra’ayin jama’a ta waya, kwanaki 40 kaffin ranar zabe. 

Yan takarar shugabancin kasa a jumhuriyar Nijar
Yan takarar shugabancin kasa a jumhuriyar Nijar RFI Hausa